USAID/NIGERIA
Ilimi shi ne ginshiƙin cigaban kowace al'umma.
2016 · 104 pages

Abstract
Matukar yara ba su iya karatu da rubutu ba, to kuwa babu wata nasara da za a samu ta fuskar ilimi. Shi kuma iya karatu ba daga sama ake samunsa ba, ba kuma tsintarsa ake yi ba. Yara suna koyon karatu ne idan an bi wata tsararriyar hanya da wasu suka sadaukar da kai domin tabbatar da ita, sannan kuma iyaye da sauran jama'ar gida suke bayar da tasu gudunmawar. Binciken da aka gudanar kwana nan a kan iya karatun yara da ke azuzuwa biyu da uku ya tabbatar da cewa, yara kalilan ne suka iya karatun Hausa a matakan farko na ilimi. Muna sane da cewa akwai bukatar jihohinmu su dauki matakan inganta kwarewar malamanmu cikin gaggawa, yadda za su iya gabatar da darussan koyon karatu a wannan mataki mai muhimmanci a rayuwarsu ta neman ilimi. An tsara wannan shiri na 'Mu Karanta!' a kan dabarun koyarwa na zamani da duniya ta aminta da shi. Kuma ya haɗa ƙwararru da muke da su daga jihohi da kuma ƙasa baki ɗaya a fannin ilimi da harshen Hausa. An samar da waɗannan littattafan ne bisa tsarin ƙumshiya da daidaituwar dabarun Karatu a Matakin Farko. An ƙarfafa tsari da dabarun Karatu a Matakin Farko ta hanyar rubuta littafin 'Mu Karanta' wanda ya haɗa da Littafin Dalibai aji 1-3 da kuma Jagoran Malamai aji 1-3. Littattafan 'Mu Karanta' na ɗalibai da jagoran malamai an samar da su ne bisa dabarun karatu kamar haka: Sanayyar Sauti, Tsarin sauti/haruffa, Gaɓar kalma/kalma, Ƙwarewa da naƙaltar karatu, Auna fahimta, Dabarun ɗab'i da Zubin rubutu. An ba wa ɗalibai damar amfani da darussan da suka koya, da kwatanta aiwatar da dabarun da suka koya. Haka kuma Littattafan Karatu a Matakin Farko suna bayar da damar bitar darussa a kullum ko a mako-mako. Littattafan suna ba wa yara damar gwaji da yin karatu matuƙa, wanda wannan yana ƙara ƙarfafashi wajen ƙwarewa da naƙaltar karatu wanda kuma wannan zai sa yara su gina ɗabi'un karatu nagari. Ina mai matuƙar farin cikin miƙa ɗimbin godiya ga Shirin nan na bunƙasa ilimi a arewacin Najeriya (Northern Education Initiative Plus) saboda kawo wannan sabon yunƙuri tare da gode wa Hukumar USAID wadda ta bayar da taimakon kuɗi da tallafin aiki.
Connected topics
Classification